Home Labarai Buhari Ya Sa Hannu A Kan Dokar Kara Kudin Kiran Waya

Buhari Ya Sa Hannu A Kan Dokar Kara Kudin Kiran Waya

150
0

Shugaban kasa Muhammadu, ya sa hannu a kan sabuwar dokar karin kudaden haraji ga masu kiran waya a Nijeriya.

Wannan, ya na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da fadar shugaban kasa ta fitar, inda ta ce za a yi karin kwabo 1 a kan kowanne kira da dan Nijeriya zai yi.

Sanarwar, ta ce za a yi amfani da kudaden ne wajen taimaka wa gajiyayyu da kuma tsamo tattalin arzikin Nijeriya daga mawuyacin halin da ya ke ciki.

Tuni dai ‘yan Nijeriya sun fara yi wa sabuwar dokar bore, inda su ke ganin kamata ya yi a rage wa dan Nijeriya harajin da ya ke biya ba wai a kara ma shi ba.