Kwanaki shida kafin saukar sa daga mulki, shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar babban titin Kano zuwa Kaduna da kuma katafariyar Gadar Neja ta biyu da wasu manyan ayyukan raya kasa guda shida.
Haka kuma, shugaba Buhari ya kaddamar da sabon ginin Helkwatar Hukumar yaki da fasa-kwauri ta Nijeriya da ke Abuja.
Mai taimaka wa shugaban kasa ta fuskar yada Labarai Femi Adesina, ya ce ya Buhari kaddamar da titin Kano zuwa Kaduna mai nisan kilomita 200, wanda gwamnatin sa ta gyara da kuma gadar Neja ta biyu da aka kirkira shekaru 16 da su ka gabata ya kuma ya sanya mata sunan sa.
Daga cikin manyan ayyuka bakwai da Gwamnatin Buhari ta kammala dai akwai gine-ginen Sakatariyar Gwamnatin Tarayya guda uku da manyan gadoji uku da kuma aikin titin.
Sauran gadojin sun hada da ta Loko zuwa Oweto, wadda ta ratsa Kogin Benue ta hade jihohin Benue da Nasarawa da kuma Gadar Ikom da ke Jihar Cross River.














































