Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bayyana
dalilin da ya hana shi halartar taron kwamitin zartarwa na
jam’iyyar APC na ƙasa.
Ya ce ya aike wa jam’iyyar saƙon neman uzuri domin samun damar halartar wasu abubuwa da ya tsara yi kafin sanarwar taron.
Tsohon shugaban ƙasar, ya kuma jaddada goyon baya ga jam’iyyar APC da kuma fatan za a kammala taro lafiya.
A na shi bangaren, shi ma tsohon mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbajo, ya aike da irin wannan saƙo na neman uzuri, kamar yadda mai magana da yawun sa Laolu Akande ya sanar.
Akande ya ce Osinbajo baya Nijeriya, don haka ba zai samu damar halartar taron ba, kuma tuni ya sanar da jam’iyyar dalilan sa.