Home Labaru Boko Haram: Rundunar Soji Ta Sake Kwato Kauyen Fadama A Jihar Adamawa

Boko Haram: Rundunar Soji Ta Sake Kwato Kauyen Fadama A Jihar Adamawa

629
0
Sojoji Sun Kashe Mahara Sama Da 100 A Dazuzzukan Zamfara Da Katsina

Rundunar sojin Nijeriya, ta ce dakarun Operation Lafiya Dole a karamar hukumar Madagali da ke jihar Adamawa sun yi gagarumar nasara a kan yan ta’addan Boko Haram a yankin.

Jami’in yada labarai na rundunar sojin Nijeriya Aminu Iliyasu ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja.

Kanar Iliyasu, ya ce an samu nasarar ne a lokacin da sojoji su ka gudanar a ayyukan kakkabe sauran mayakan Boko Haram da ISWAP daga Madagali da Waga Lawan, da Jaje da Fadama Ukka a karamar hukumar Madagali na jihar Adamawa.

A cewar sa, an lallasa sauran ‘yan ta’addan ba da wasa ba, inda aka tursasa su tserewa daga yankin.

Kayayyakin da aka kwato daga ‘yan ta’addan sun hada da kekuna biyu, da kwafin Qur’anai da sauran abubuwa da dama, amma cikin ikon Allah babu wanda ya mutu daga bangaren sojoji.