Home Labaru Bidiyon Cin Hanci: Kotu Ta Yi Watsi Da Karar Aka Shigar A...

Bidiyon Cin Hanci: Kotu Ta Yi Watsi Da Karar Aka Shigar A Kan Ganduje

423
0
Abdullahi Ganduje, Gwamna jihar Kano
Abdullahi Ganduje, Gwamna jihar Kano

Babbar kotun tarayya da ke Kano, ta yi watsi da karar da wani lauya mai rajin kare hakkin bil’adama Bulama Bukarti ya shigar dangane da zargin gwamna Ganduje da karbar cin hanci.

Bukarti dai ya nemi kotun ta tilasta wa hukumar EFCC ta binciki zargin da ake yi wa Ganduje, bisa karbar cin hancin dalar Amurka miliyan biyar kamar yadda wani faifan bidiyo ya nuna.

Alkalin kotun mai shari’a Obiorah Egwuatu, ya ce kotun ta yi watsi da karar ne saboda rashin gabatar da hujja daga bangaren mai kara.

A takardar karar da ya shigar, Bukarti ya bukaci kotun ta bada umarnin da zai tilasta EFCC ta gudanar da bincike ta hanyar amfani da kimiyyar zamani, domin tabbatabar da cewa fuskar Ganduje ce a cikin faifan bidiyon ko akasin haka.

Yayin yanke hukuncin, mai shari’a Egwuatu ya ce babu wata hujja mai karfi da mai kara ya gabatar domin jingina bukatar sa ta neman a ba EFCC umarnin gudanar da bincike a kan faifan bidiyon.

Leave a Reply