Home Labarai Beli: Kotu Ta Bayar Da Yahaya Bello Kan Kudi Naira Miliyan 500

Beli: Kotu Ta Bayar Da Yahaya Bello Kan Kudi Naira Miliyan 500

73
0
Yahaya Bello (1)
Yahaya Bello (1)

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da belin tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello kan kuɗi naira miliyan 500.

A zaman da kotun ta yi a ranar Juma’a ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Emeka Nwite, kotun ta buƙaci ya gabatar da mutum biyu da za su tsaya masa domin samun belin.

Alƙalin ya ce dole ne mutanen da za su tsaya masa su kasance sun mallaki kadarori a Abuja, babban birnin tarayya.

Haka kuma kotun ta ce dole ne ma su tsaya masan su gabatar wa kotun takardun kadarorin nasu domin tantancewa.

A baya-bayan nan ne dai hukumar EFCC ta gurfanar da tsohon gwamnan na Kogi a gaban kotu bisa zarge-zarge 19 da suka ƙunshi almundahanar kuɗaɗe da yawansu ya kai naira biliyan 80.

Leave a Reply