Ana zaben shugaban kasa, bayan mutuwar Ebrahim Raisi a wani hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a watan jiya.
Jagoran juyin-juya-halin Musulunci na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya yi kira ga jama’a su yi fitar farin dango,
yayin da ake tunanin jama’a da dama za su kauracewa zaben.
Akwai ‘yan takara hudu, ciki har da wanda ake kallo a matsayin mai ra’ayin kawo sauyi, Massoud Pezeshkian.
Wakiiliyar BBC ta ce sanya sunan sa na iya sa wa a samu fitar masu kada kuri’a, sannan abu ne da zai sa a sake mancewa da Iran.
Sauran su ne kakakin majalisar dokokin Iran, da tsohon mai shiga tsakani na nukiliyar kasar Saeed Jalili, da kuma wani malami Mostafa Mohammadi.














































