Shugaban Uganda Yoweri Museveni ya ce soma amfani da kamfanonin ma’adinin coal da kasashen nahiyar Turai ke yi, a daidai lokacin da ake fuskantar karancin makamashi abin mamaki ne game da burin kasashen na cimma muradun sauyin yanayi.
Daddaden shugaban kasar ya kuma soki sabbin dokokin da suka bayar da dama ga kasashen yamma wajen zuba jari a fannin ma’adinan makamashi a Afirka.
Sharadin zuba jarin shi ne sai idan za a fitar da Man fetur da albarkatun iskar gas zuwa kasashen na Turai, abin da kuma shugaban ya kira ‘tsantsar munafurci’
Yoweri Museveni, ya wallafa a shafin sa cewa ba za a amince da ikirarin samar mana da ci gaba ba bayan su kuma sun cimma muradun kasashen su kan batun sauyin yanayi.
Ya ce kiraye-kirayen da ake yi wa kasashen Afirka su rungumi amfani da makamashin da ba ya gurbata muhalli bai bar mu da komai ba sai rashin wutar lantarki.
Ya kara da cewa rashin cimma muradun sauyin yanayi da kasashen Turai suka yi, ba zai zama matsala ga Afirka ba.
You must log in to post a comment.