Hukumar Tattara Bayanan Sirri ta Ƙasa NIA, ta ce, Kotun Ɗaukaka Ƙara ba ta maida Mohammed Dauda a kan kujerar Darakta-Janar na hukumar ba kamar yadda wasu kafafen yaɗa labarai su ka bayyana.
A Cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja, Shugaban sashen shari’a na hukumar Mista A. H. Wakili, ya ce ba gaskiya ba ne cewa an maida Mohammed Dauda a kan muƙamin shugabancin hukumar.
Sanarwar ta ce, an ja hankalin hukumar akan wani rahoton da ba daidai ba, inda aka yaɗa a shafin yanar gizo dangane da maida Ambasada Mohammed Dauda matsayin Darakta-Janar na Hukumar.
Ta ce asali Mohammed Dauda ba tabbataccen Darakta-Janar na hukumar ba ne, an dai naɗa shi ne na wucin-gadi bayan ƙarewar wa’adin Ambasada Ayo Oke, bayan kuma Ambasada Arab Yadam ya yi riƙon ƙwarya na ɗan lokaci, har sai da Shugaba Buhari ya naɗa Ambasada Ahmed Rufa’i Abubakar a matsayin tabbatacce Darakta-Janar.
Sanarwar ta ƙara da cewa, a bayyane ta ke cewa labarin da aka yaɗa shiryayyen lamari ne a tsakanin Mohammed Dauda da muƙarraban sa domin a kawar da hankalin jama’a.