Home Labarai Bashin Albashi: Ana Taƙaddama Tsakanin Mbappe Da PSG

Bashin Albashi: Ana Taƙaddama Tsakanin Mbappe Da PSG

30
0
Kylian Mbappe Future world football legend
Kylian Mbappe Future world football legend

Hukumar ƙwallon ƙafa ta Faransa ta yi watsi da buƙatar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta PSG kan ta sake duba umarnin da ta ba ƙungiyar umarnin cewa ta biya ɗan wasan gaban, Kylian Mbappe, bashin sama da dala miliyan 57.

Wannan ya biyo bayan wata zazzafar taƙaddama tsakanin ɗanwasan wanda yanzu yake taka leda a ƙungiyar Real Madrid.

Ɗanwasan yana ikirarin cewa yana bin PSG bashin albashi da wasu alawus, wanda ita kuma ƙungiyar ta ce ya amince zai yafe mata kuɗin idan ya tafi Real Madrid a matsayin kyauta.

Matashin ɗanwasan ya koma Real Madrid ne a matsayin kyauta bayan kwantiraginsa da PSG ya ƙare.

Ita dai PSG ta dage ba za ta biya bashin a yadda yake, wanda hakan ke nufin yanzu maganar a kotu za ta ƙare.

Leave a Reply