Home Labaru Kasuwanci Bankin Nijeriya Ya Samar Da Ma’Aikacin Mutum-Mutumi A Bankin

Bankin Nijeriya Ya Samar Da Ma’Aikacin Mutum-Mutumi A Bankin

120
0

Bankin First Bank na Nijeriya, ya ƙaddamar da wani mutum-
mutumin ma’aikacin banki a reshen sa na Adetokunbo
Ademola da ke Legas domin kula da koken masu ajiya a
bankin.

Shugaban rukunin bankuna da kasuwanci da hulɗar kamfanoni na bankin Ani-Mumuney ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar.

Ya ce mutum-mutumin ya na da girkakkiyar kyamarar daukar hoton bidiyo da fasahar na’ura mai ƙwaƙwalwa, wanda zai maida shi tamkar ɗaya daga cikin ma’aikata masu fara’a na reshen bankin.

Wannan dai wani yunquri ne irin sa na farko da bankin ya yi domin ganin an habbaka harkar banki a Nijeriya.

Mista Ani ya kar da cewa, mutum-mutumin ya na ɗauke da bidiyo na harkar banki da fasahar zamani, kuma ya na mu’amala da masu ajiya ta hanyar yin hira da su, sannan ayyukan da zai rika yi sun haɗa da warware matsalolin masu ajiya da su ka shafi ajiyar kuɗi da fitar da kuɗi da matsalar katin ATM.

Leave a Reply