Home Labarai Bankin China Ne Zai Samar Da Kuɗin Gina Layin Jirgin Zuwa Kano

Bankin China Ne Zai Samar Da Kuɗin Gina Layin Jirgin Zuwa Kano

373
0
Gwamnatin tarayya ta ce za ta samar da jami’an tsaro na musamman, wadanda za su riƙa kula da sufurin jiragen ƙasa a wani ɓangare na matakan magance hare-haren da ake kai wa jiragen da fasinjoji.

Majalisar dattawa ta amince wa Bankin raya ƙasa na China ya
samar da kuɗaɗen da za a yi amfani da su wajen gina layin
dogo da zai ci akalla dala biliyan ɗaya.

Tun farko dai an shirya da wata cibiyar samar da rance a China, domin samar da kuɗin da za a yi amfani da su wajen gina layin dogo daga Kaduna zuwa Kano, amma sai cibiyar ta janye daga yarjejeniyar a shekara ta 2020.

Lokacin da ya hau mulki shekaru takwas da su ka gabata, Shugaba Buhari ya ba da fifiko wajen inganta hanyoyin sufuri da inganta ayyukan samar da wutar lantarki, amma duk da haka samar da kuɗaɗe ya kasance babban cikas wajen gudanar da ayyukan.

Majalisar dai ta amince a ciyo bashin biliyoyin dala daga China da sauran masu bada rance na ƙasashen duniya, amma har yanzu kuɗaɗen ba su samu ba.

LEAVE A REPLY