Home Labarai Babban Layin Lantarki Na Najeriya Ya Faɗi Karo Na 11 A 2024

Babban Layin Lantarki Na Najeriya Ya Faɗi Karo Na 11 A 2024

249
0
125448769 1cd84aa7 af14 4126 ae61 0d2c66a55af9
125448769 1cd84aa7 af14 4126 ae61 0d2c66a55af9

Babban Layin Wutar Lantarkin Najeriya, ya sake faɗuwa karo na 11 a shekarar 2024.

Wannna na cikin wata sanarwa da Hukumar Gudanar da Tsarin Wutar Lantarki ta Ƙasa (ISO), reshen Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Najeriya (TCN), ta fitar.

Ta ce dukkanin tashoshin da ke rarraba wutar sun daina aiki tun daga ƙarfe 2 na rana.

Kafin haka, misalin karfe 1 na rana, tashoshin suna samar da kimanin megawatt 3,087 na wutar lantarki.

Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Jos (Jos Disco), ya tabbatar da faruwar matsalar cikin wata sanarwa da ya fitar.

Sanarwar ta ce: “Rashin wutar lantarkin da ake fuskanta a yankunanmu ya faru ne sakamakon katsewar wuta daga babban layin rarraba wuta ta ƙasa.

“Wannan katsewa ta faru ne a ranar Laraba, 11 ga wata Disamba, 2024, da misalin ƙarfe 1:33 na rana, wanda ya haifar da rashin wuta a dukkanin manyan layukanmu.”

Sanarwar ta ƙara da cewa: “Muna aiki tuƙuru domin gyara wutar lantarki yadda ta ke a baya. Muna godiya da haƙurinku da fahimtarku yayin da muke ƙoƙarin yi muku hidima.”

Leave a Reply