Kwamitin ayyuka na kasa na jam’iyyar PDP, ya gana da ‘yan takarar gwamna na jam’iyyar 36.
Taron dai ya samu halartar daukacin ‘yan takarar gwamna na jam’iyyar PDP in ban da gwamnan jihar Oyo Seyi Makinde da ke hutu a kasar waje, yayin da Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya aike da sakon ban-hakuri.
Wata majiya ta ce, taron na sirri ne da ke da nasaba da zaman tattaunawa tsakanin shugabannin jam’iyyar na kasa da ‘yan takarar jam’iyyar gabanin zaben shekara ta 2023.
Taron dai ya na zuwa ne, a daidai lokacin da ake kira ga shugaban Jam’iyyar na kasa Dokta Iyorchia Ayu ya sauka daga shugabanci, kamar yadda Nyesom Wike ya gindaya sharuddan warware takaddamar zaben gwamnan jihar Delta Ifeanyi Okowa a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar PDP.














































