Home Labaru Ba Zan Maida Wani Yanki Na Nijeriya Saniyar-Ware Ba – Tinubu

Ba Zan Maida Wani Yanki Na Nijeriya Saniyar-Ware Ba – Tinubu

100
0

Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya yi
alƙawarin yi wa ƙasa ayyukan ci-gaba daidai gwargwado ba
tare da nuna wariya ga wani bangare na Nijeriya ba.

A wata sanarwa da mai taimaka ma shi ta fuskar yada labarai Abdulaziz Abdulaziz ya fitar, Tinubu ya bayyana haka ne yayin ziyarar aiki ta kwanaki biyu da ya kai jihar Rivers, domin ƙaddamar da ayyukan da gwamnatin Nyesom Wike ta aiwatar.

Tinubu ya ce ba zai maida wani yanki tamkar saniyar-ware ba, hasali ma zai bar ayyukan da ba za a manta da su ba a faɗin Nijeriya.

A karshe ya gode wa gwamna Wike da al’ummar jihar Rivers bisa goyon bayan da su ka ba shi, ya na mai cewa ba zai taɓa mantawa da muhimmiyar rawar da su ka taka ba a yaƙin neman zaɓen da ya yi har ya samu nasarar zama shugaban ƙasa.

Leave a Reply