Home Labaru Ba Mu Yarda Da Tsarin Raba Shugabancin Majalisun Tarayya Ba – Akeredolu

Ba Mu Yarda Da Tsarin Raba Shugabancin Majalisun Tarayya Ba – Akeredolu

104
0

Gwamnan Jihar Ondo Rotimi Akeredolu, ya yi fatali da tsarin
raba mukaman shugabancin Majalisun Tarayya, wanda
jam’iyyar APC da Bola Ahmed Tinubu su ka amince da shi.

Rotimi Akeredolu, ya bayyana tsarin a matsayin wanda ke tattare da rashin adalci, kuma ya saba wa tsarin raba-daidai da jam’iyyar su ke jagoranci wajen ganin kowane bangare ya shiga an dama da shi a tafiyar dimokuradiyar Nijeriya.

Akeredolu, ya ce abin takaici ne yadda shiyyar Arewa maso Yamma ta samu manyan kujeru biyu a majalisa, yayin da wasu yankuna ba su da mukami ko guda ba.

Ya ce na farko ba a yi tsari mai kyau ba wajen gabatar da mutanen da aka tsaida a matsayin shugabanni ba tare da tuntuba da kuma dogon nazari ba, sannan aka yi watsi da sauran ‘yan takarar da ke neman shugabancin ba tare da neman amincewar su ba.

Akeredolu, ya kuma bayyana matakin a matsayin wata gadar- zaren da ake shirya wa Bola Ahmed Tinubu, domin ganin shugabancin sa ya samu matsala tun daga matakin farko.

Leave a Reply