Masu adawa da zaɓin Tajuddeen Abbas a matsayin wanda jam’iyyar APC ta zaɓa ya zama kakakin majalisar wakilai na Kungiyar G7, sun ce su nan a kan bakan su cewa ba za su amince da zaɓin Tinubu da APC ba.
Kungiyar, wadda ta kunshi mataimakin kakakin majalisar wakilai Idris Wase, da Yusuf Gagdi da Mukhtar Betara da Sada Soli da Aminu Jaji da Mariam Onouha, sun yi ganawa ta musamman a masaukin baki na Transcorp da ke Abuja.
Jim kadan bayan kammala taron ne, Sada Soli ya bayyana wa manema labarai cewa ba za su bi zaɓin jam’iyyar APC ba, don haka a cikin makon da za a shiga za su sanar da ɗan takarar da dukkan su da magoya bayan su za su mara wa baya, amma ba za su bi wanda Tinubu da APC su ka ƙaƙaba masu ba.
A na shi bangaren, Yusuf Gagdi ya ce za su bayyana sunayen wadanda su ke so su zama kakakin majalisa da mataimakin sa, domin ba za su zura ido su na gani a yi ma su ƙarfa-ƙarfa a kan abin da ba haka ba.