Home Labarai Ayyukan Jinkai: Za Mu Raba Wa Jami’An Tsaro Tallafin Abinci —Gwamnan Kano

Ayyukan Jinkai: Za Mu Raba Wa Jami’An Tsaro Tallafin Abinci —Gwamnan Kano

41
0

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya ce nan ba da
jimawa ba gwamnatinsa za ta fara rabon tallafin kayan
abinci ga talakawa, da jami’an tsaron da ke Jihar.


Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin taron bude-baki da jagororin tsaro a Gidan Gwamnatin jihar, inda ya yaba wa jami’an bisa kokarin da suke yi na tabbatar da tsaro da walwalar Kanawa.

A cewar kakakinsa Sunusi Bature Dawakin Tofa, Gwamnan ya kuma jadadda kudirinsa na ci gaba da kare dukiya da rayukan al’ummar Kano a kokarin sauke nauyin da Allah Ya dora masa.


Abba ya kuma yaba wa Shugaba Bola Tinubu, bisa amincewa da rabon kayan abincin da ya ce za a fara a fadin jihar nan ba da
jimawa ba .


Kazalika, ya bukaci jami’an tsaron da su dage wajen yi wa jihar da kasa baki daya addu’a a wannan watan na Ramadan, domin
tabbatuwar zaman lafiya da kwanciyar hankali.


Wadanda suka halarci buda-bakin dai sun hada da Kwamishinan ’Yan Sandan jihar CP Muhammad Hussaini Gumel, Birgediya Janar M.A Sadiq na Rundunar Sojin Najeriya da ke Barikin Bukavu a Kano da sauransu.

Leave a Reply