Home Labarai Ayyukan Gina Kasa: Shugaban Kasa Buhari Ya ce Gwamnatinsa Ta Yi Rawar...

Ayyukan Gina Kasa: Shugaban Kasa Buhari Ya ce Gwamnatinsa Ta Yi Rawar Gani 

402
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa ta yi namijin kokari, idan aka yi la’akari da dan abin da take samu wurin tafiyar da lamuran kasa.

Shugaban kasa ya yi wadannan kalaman ne yayin da yake jawabi a gidan gwamnatin jihar Imo da ke birnin Owerri bayan bude wasu manyan ayyuka da Gwamna Hope Uzodinma ya yi.

Shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa ta yi kokarin gudanar da ayyuka da dama duk da kudaden da take samu ba basu isa.

Ya kuma jinjina wa gwamnatinsa bisa nasarar da ta samu na gurgunta kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram a Kudu maso Gabas, a rikicin da ya ce ya gada daga gwamnatin PDP a 2015.

Shugaban ya kuma yi jinjina ga gwamnan jihar ta Imo kan gayyatar shi a karo na biyu cikin shekara daya don ya bude ayyukan da ya aiwatar.

Leave a Reply