Home Home An Rantsar Da Sabbin Alƙalan Kotun Ma’aikata Shida

An Rantsar Da Sabbin Alƙalan Kotun Ma’aikata Shida

257
0

Shugaban alƙalan Nijeriya Mai Shari’a Olukayode Ariwoola ya rantsar da sabbin alƙalai shida na Kotun Ma’aikata, wanda ya a Kotun Ƙolin Nijeriya da ke birnin tarayya Abuja.

Yayin rantsarwar, Mai Shari’a Ariwoola ya yi kira ga sabbin alƙalan su yi aikin da ya rataya a wuyan su a kan gaskiya da martabawa daidai da tanadin dokar ƙasa.

Ya ce ɓangaren shari’ar Nijeriya ya na buƙatar maza da mata masu nagarta, waɗanda za su kwatanta gaskiya ga ‘yan ƙasa ba tare da tsoro ko tausayi ba.

Mai Shari’a Ariwoola, ya kuma nusar da alƙalan su sa ran fuskantar manyan shari’o’i masu yawa, waɗanda ka iya zuwa tattatare da ƙalubale, ya na mai gargadin su da cewa in ban da halaka babu abin da rayuwa da dukiyar da aka tara ta haramtacciyar hanya ke jefa mutane. Ya ce babu wani ma’aikacin shari’a da zai bari a tozarta ɓangaren shari’ar Nijeriya, ya na mai cewa ba zai yiwu a yi wannan tafiya mai dogon zango sannan a ce an gaza ba.

Leave a Reply