
Jami’an ‘yan sanda na birnin tarayya Abuja, sun tabbatar da mutuwar mutum ɗaya a wani rikicin kabilanci da ya ɓarke a unguwar Gwarimpa.
Mai magana da yawun rundunar yan sanda ta Abuja SP Josephine Ade, ta ce rikicin ya ɓarke ne tsakanin wasu ƙabilu biyu mazauna wani yanki da ake kira Gwarimpa village.
Bayanai sun ce tun ranar Asabar da ta gabata ne tarzomar ta fara, bayan ƙabilar Gbagyi sun yi yunƙurin korar wasu da su ke zargin su na dillancin ƙwayoyi a yankin.
‘Yan sanda sun ce mutumin da aka kashe matashi ne ɗan shekara 20, kuma ya rasu ne sanadiyyar raunukan da aka ji ma shi, kuma rikicin ya sake tashi da safiyar Litinin din nan, bayan Hausawa sun samu labarin rasuwar ɗan’uwan su da aka kai asibiti.
SP Josephine ta ce ba gaskiya ba ne jita-jitar da ake yaɗawa, cewa Fulani makiyaya ne su ka kai hari a unguwar Gwarimpa, yayin da wasu kafafen yaɗa labarai su ka bada rahoton cewa rikicin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane uku, zargin da mai magana da yawun ‘yan sandan ta ce shi ma babu ƙamshin gaskiya a ciki.













































