Kamfanin man fetur na Nijeriya NNPC, ya kara farashin litar
man fetur zuwa Naira 540 a hukumance.
Mai Magana da yawun kamfanin NNPC Garba Deen Muhammad ya tabbatar da Karin farashin a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce dokar sabon farashin man za ta fara aiki ne daga ranar 31 ga watan Mayu na shekara ta 2023.
Kamfanin NNPC, ya ce farashin man fetur a Maiduguri ya koma naira 557 a kan kowacce lita, yayin da a Yobe da sauran jihohin Arewa maso Gabas farashin ya tasamma naira 550 a kan kowace lita.
Birnin Kebbi da sauran jihohin Arewa maso Yamma kuma za su sayi litar man fetur a kan naira 545, A yankin jihohin Arewa ta Tsakiya kuma farashin ya tsaya a kan naira 537 a kan kowace lita, sai dai a Illorin kuma farashin litar man ya tsaya a kan naira 515.
Sanarwar ta ce, Kudu maso Kudancin Nijeriya za su sayi litar mai a kan naira 520, yayin da sauran jihohin Kudu maso Kudufarashin litar mai ya tsaya a kan naira 511.