Home Labaru An Halaka Mutum Takwas Da Ƙona Gidaje A Filato

An Halaka Mutum Takwas Da Ƙona Gidaje A Filato

43
0

‘Yan bindiga sun shiga kauyen Wumat da ke karamar hukumar Bokkos ta jihar Filato tare da kashe mutane 8 da kuma jikkata wasu da dama.

Mazauna kauye sun shaida wa manema labarai cewa, ‘yan bindigar sun kuma koma kone gidaje akalla 20.

Wani mazaunin Bokkos mai suna Adamu Isa, ya ce ‘yan bindigar sun harbe mutane 8, kuma yanzu haka akwai mutanen da su ka jikkata a asibiti.

Har yanzu dai ‘yan sanda ba su tabbatar da harin ko fitar da karin haske ba.