Home Labaru An Fara Yi Wa Aso Rock Kwaskwarima Gabanin Rantsar Da Tinubu

An Fara Yi Wa Aso Rock Kwaskwarima Gabanin Rantsar Da Tinubu

106
0

Yayin da ake shirin rantsar da zababben shugaban kasa Bola
Ahmed Tinubu, yanzu haka an fara yi wa fadar shugaban kasa
kwaskwarima domin samar da kyakkywan yanayi ga shugaba
mai jiran gado.

Tuni dai kwararrun ma’aikata da masu fanti sun dukafa wajen gyare-gyare da fantin bangayen ginin fadar shugaban kasa, a wani kokari na shirye-shiryen mika mulki ga sabon shugaba.

Mai magana da yawun shugaban kasa Garba Shehu ya bayyana haka a shafinsa na Instagram.

Garba Shehu, ya ce yanzu haka ana kan gyaran fadar shugaban kasa, inda masu fanti ke ta faman aiki domin ganin ta yi kyan gani ga shugaba mai jiran gado.

Leave a Reply