Home Home An Ƙi Bayar Da Gawar Wani Mutum A Asibiti Kan Zargin ‘Yan’uwan...

An Ƙi Bayar Da Gawar Wani Mutum A Asibiti Kan Zargin ‘Yan’uwan Sa Da Dukan Likita

37
0

Hukumomin asibitin koyarwa da ke Ilorin a jihar Kwara, sun ƙi bada gawar wani mutum tare da kama ɗaya daga cikin ‘yan’uwan sa, bisa zargin dukan wani likitan asibitin.

Rahotanni sun ce, uku daga cikin ‘yan’uwan mamacin mai suna Alhaji Saliu ne su ka bugi wani likita a sashen kula da masu buƙatar kulawar gaugawa, saboda abin da su ka kira rashin kula da lilitocin su ka nuna masu.

 Lamarin dai ya faru ne, jim kaɗan bayan rasuwar ɗan’uwan nasu da ya yi fama da cutar sankarar jini.

Ɗaya daga cikin ‘yan’uwan mamacin, ya ce asibitin ya hana su gawar mamacin saboda faruwar lamarin.

Shugabar ƙungiyar likitoci reshen asibitin Mrs. Elizabeth Ajiboye ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce gamayyar ƙungiyar likitoci ta Nijeriya ne su ka umarci hukumomin asibitin kada su bada gawar mamacin, har sai an kama tare da gurfanar da mutanen da su ka bugi likitan a gaban kotu’.