Home Labarai Amurka Za Ta Taimaka Wa Najeriya Magance Matsalolin Yanayi 

Amurka Za Ta Taimaka Wa Najeriya Magance Matsalolin Yanayi 

104
0


Gwamnatin Amurka ta yi alkawarin tallafa wa Najeriya wajen magance matsalar sauyin yanayi da ta muhalli da take fama da su.

Wakilin Shugaban Amurka na Musamman, Mista John Kerry ne ya bayyana hakan, a wani zauren tattaunawa da manema labarai ranar Talata a Abuja, Babban Birnin Tarayyar Najeriya.

Kerry ya kuma yaba wa Shugaba Buhari, bisa kokarinsa na samar da shirye-shirye da ayyuka na musamman da za su rage matsalolin yanayi da muhalli a Najeriya.

Ya kara da cewar babban cigaba ne shugaban ya samar a Najeriya kan sauyin yanayi, kuma ya ji dadin yadda ya ga shirye-shiryen da gwamnatin tarayya ke yi domin kawo karshen matsalar.

Ya kara da cewa, “Idan aka cim-ma hakan, ba Najeriya kadai ba, duk duniya ma za ta amfana.”

Kerry ya ce dimbin albarkatun man fetur da iskar gas da kasar ke da su ne ya taimaka wajen jefa ta a matsalar yanayin da muhalli.

Leave a Reply