Jami’ai a gabashin Afghanistan sun ce aƙalla mutum 40 ne suka rasa rayukan su sakamakon mamakon ruwan saman da aka yi da ya haddasa ambaliyar ruwa.
Jami’an sun ce akwai wasu kusan 350 kuma da suka samu rauni.
Jami’in hukumar agajin gaggawa na yankin sun ce mamakon ruwan sama gami da tsawar da aka yi a lardin Nangahar
ranar Litnin da tsakar dare ya lalata gidaje 400.