Al’ummomin Masarautar Arak da ke karamar hukumar Sanga ta jihar Kaduna, sun bayyana damuwa a kan dakatar da sarkin su Birgediya Janar Iliya Aliyu Yammah mai ritaya da tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa’i ya yi.
A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban rikon kwarya na kungiyar ci-gaban al’ummr Numana Kwamred Ahmed Manzo, mutanen sun bayyana sauke sarkin a matsayin rashin adalci.
A wani sakon taya murna da su ka aike wa sabon gwamnan jihar Kaduna Malam Uba Sani, sun bukaci ya sake yin nazari a kan matakin tare da maida basaraken a kan mukamin sa.
Idan dai za a iya tunawa, gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da dakatar da basaraken ne a cikin wata sanarwa da kwamishinar kula da harkokin kananan hukumomin jihar Kaduna Umma Ahmed ta fitar a ranar 22 ga watan Mayu na shekara ta 2023.
A karshe mutanen sun rokin gwamna Uba Sani ya sake duba ga lamarin bisa adalci, sannan ya maida basaraken a kan mukamin sa kamar yadda al’ummar sa su ka bukata.














































