Home Labarai Almundahana A Kasafin 2024: Gwamnatin Tinubu Ta Musanta Coge A Kasafin Kuɗin...

Almundahana A Kasafin 2024: Gwamnatin Tinubu Ta Musanta Coge A Kasafin Kuɗin Ƙasar

117
0

Fadar shugaban Najeriya ta musanta zargin yin coge a kasafin kudin 2024 wanda shugaban kasa ya sanyawa hannu a watan Janairu.

Ɓangaren zartarwar ta mayar da martani ne kan wata hira da shugaban ƙungiyar ƴan majalisar dattawa na yankin arewa, Sanata Abdul Ningi ya yi wanda zargin cewa kasafin kuɗin da bangaren zartarwa ke aiki da shi ba shi ne majalisun dokokin kasar nan suka rattabawa hannu ba.

Sai dai mataimaki na musamman ga shugaban kan watsa labarai, Abdulaziz Abdulaziz ya ce ba kamshin gaskiya a zargin.

Leave a Reply