Home Home Akwai Akalla Yara Miliyan 2 Da Ba A Taba Yi Musu Allurar...

Akwai Akalla Yara Miliyan 2 Da Ba A Taba Yi Musu Allurar Riga Kafi Ba A Najeriya – UNICEF

311
0
Asusun kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya UNICEF, ya ce an gano akalla kananan yara miliyan 2 da dubu 300 da ba su taba yin allurar riga-kafi ba a Nijeriya, daga shekara ta 2019 zuwa 2021.

Ta ce ya zuwa yanzu akwai kananan yara miliyan 67 da ba su yi allurar riga-kafi ba a duniya, inda a ciki akwai yara miliyan 48 da ba su taba yin allurar ba daga shekarun 2019 zuwa 2022.

Asusun ya kara da cewa, baya ga yara miliyan 68 din da ba su yin allurar riga-kafin ba, an kuma gano cewa yi wa kananan yara allurar rigakafi ya fara yin kasa a kasashe 112 na duniya.

Jami’in lafiya na Asusun Eduardo Celades, ya ce Nijeriya ita ce kasa ta biyu baya ga India a jerin kasashen duniya da su ka fi yawan yaran da ba su yi allurar riga-kafi ba.

Leave a Reply