Home Labaru Aikin Jarida Zan Koma Idan Na Sauka Daga Mulki – Gwamnan Benue

Aikin Jarida Zan Koma Idan Na Sauka Daga Mulki – Gwamnan Benue

176
0

Gwamnan Jihar Benue mai barin gado Samuel Ortom, ya ce
zai iya komawa dan jarida mai zaman kan sa bayan ya bar
karagar mulki.

Da ya ke jawabi a gidan talabijin na Arise game da shirye- shiryen sa bayan ya sauka daga mulki, Ortom ya kuma zargi Fadar Shugaban Kasa da kashe makudan kudade wajen ganin bai yi nasara a zabe ba.

Ya ce ya san ko nawa aka ba Jihar Benue daga Fadar Shugaban Kasa domin tabbatar da ganin ya fadi zabe, amma ya rungumi kaddara kuma ya sha alwashin taimaka wa duk wanda ya zo a bayan sa muddin ya nemi taimakon shi.

Gwamna Ortom ya kuma yi zargin cewa Shugaba Buhari ya ciyar da Nijeriya baya, amma ya ce ya yafe ma shi duk abin da ya yi masa kamar yadda lttafin Baibul ya karantar da shi.

Sai dai Samuel Ortom ya yi fatan cewa al’amura za su inganta a gwamnatin sabon Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu.

Leave a Reply