Tsohon gwamnan jihar Zamfara Sanata AbdulAziz Yari ya raba wa akalla talakawan jihar Zamfara ragunan Layya 500.
Shugaban kwamitin rabon kayayyakin Sha’aya Sarkin-Fawa ya bayyana haka, lokacin da ya ke raba ragunan a karamar Hukumar Talatan-Mafara.
Sarkin-Fawa ya ce wannan abu ne da Abdul-Aziz Yari ya saba yi domin taimaka wa Talakawa don su samu yin Layya a wannan lokaci.
Ya ce rabon ya shafi makwafta da gidajen marasa galihu da ‘yan gudun hijira da marayu da ke cikin garin Talata-Mafara kawai, baya ga raguna dubu 1 da shanu 400 da Sanatan ya raba wa shugabannin jam’iyyar APC a baya.
A karshe Sarkin Fawa ya yi kira ga mutanen da su ka amfana da kyaututtukan su cigaba da yi wa kasa addu’a da kuma fatan Allah ya kara mana zaman lafiya da ci-gaba.














































