Home Labaru Afghanistan Ta Tsara Kasafin Kudi Ba Tare Da Tallafi Ba

Afghanistan Ta Tsara Kasafin Kudi Ba Tare Da Tallafi Ba

66
0

Duk da irin tarin matsalolin da kasar Afghanistan ke ciki, jagororin Taliban sun tsara kasafin kudin kasar na shekara mai kamawa.

A karon farko cikin shekaru 20, ma’aikatar kudin kasar Afghanistan karkashin gudanarwar gwamnatin Taliban, ta tsara daftarin kasafin kudin kasar ba tare da wani tallafin daga ketare ba.

Kakakin ma’aikatar, Ahmad Wali Haqmal, wanda bai bayyana girman kasafin kudin na Afghanistan na badi ba, ya ce sai majalisar zartarwa ta amince da shi ne za a kai ga bayyana wa kowa.

An dai tsara kasafin ne yayin da kasar ke fama da matsaloli na tattalin arziki da ma bukatar agajin jin kai.

A baya-bayan nan ne Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana karancin abinci da ake fama da shi a kasar a matsayin matsala gagaruma.