Home Labaru Kiwon Lafiya Abun Kunya: Kotu a Legas Ta Daure Uban Da Ya Yi Wa...

Abun Kunya: Kotu a Legas Ta Daure Uban Da Ya Yi Wa Ɗiyarsa Fyaɗe  Rai Da Rai

169
0

Kotu a jihar Legas ta yanke hukuncin ɗaurin rai-da-rai kan wani uba da ya yiwa diyarsa fyaɗe tare da abokinsa.

Uban da aka bayyana sunansa da Adewale Ibitoye da abokinsa Moses Oruke sun rinƙa yiwa ɗiyarsa mai shekara 14 fyaɗe har ta kai ga su sun yi mata ciki.

Mai sharia Abiola Soladoye ta yanke musu hukuncin ne bayan kotu ta tabbatar mutanen biyu sun aikata laifin da ake zarginsu da shi.

Abiola Soladoye ta yi alla-wadai da wannan kazamin cin zarafin kan ɗiyar da mutum ya haifa, la’akari da yadda suka rinƙa lalata da yarinyar na tsawon lokaci babu tausayi.

Yarinyar ta shaidawa Kotu cewa uban nata bayan shafe tsawon lokaci yana yi mata fyaɗe, sai aka kai gaɓar da ya miƙa ta ga abokinsa da sunan wai shi ne sabon mijinta tare da karɓar kwalbar giya.

Alkaliyar a kotun da ke sauraron kararraki kan cin zarafi da lalata ta bukaci a sanya sunayen mutanen a kundin rajistar kotun.

Leave a Reply