Home Labarai Abdulaziz Yari Ya Bayyana Gaskiyar Lamari Game Da Batun Sauya Shekar Sa

Abdulaziz Yari Ya Bayyana Gaskiyar Lamari Game Da Batun Sauya Shekar Sa

62
0

Tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari, ya bayyana
rahoton sauya shekar bangaren sa zuwa jam’iyyar PDP a
matsayin azarbabi.

A ranar Lahadin da ta gabata ne, shugaban jam’iyyar PDP na
jihar Zamfara, Kanar Bala Mande mai ritaya ya shaida wa
manema labarai cewa Abdul-Aziz Yari da Sanata Marafa da
sauran jiga-jigan jam’iyyar APC sun sauya sheka zuwa
jam’iyyar PDP.

Kakakin jam’iyyar APC bangaren Yari Ibrahim Magaji, ya ce
shugaban jam’iyyar PDP na jihar ya yi gaugawa wajen sanar da
lamarin.

Ya ce bisa ga hukuncin su na barin APC, sun shiga tattaunawa
da jam’iyyun siyasa da dama, amma ba su cimma matsaya da
wata jam’iyya ba.