Home Labaru Abba Ya Maida Muhuyi Magaji Kan Muƙaminsa

Abba Ya Maida Muhuyi Magaji Kan Muƙaminsa

294
0

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ya amince da maida
Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado a matsayin Shugaban
Hukumar Sauraren Korafe-korafen Al’umma da Yaki da Cin
Hanci da Rashawa ta jihar Kano domin kammala wa’adin sa.

Bayanin hakan ya na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren yada labarai na gwamnan jihar Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa.

Idan dai za a iya tunanwa, gwamnatin Abdullahi Umar Gnaduje ta dakatar da Muhuyi tare da tsige shi daga mukamin sa, bayan majalisar dokoki ta jihar ta ce ta na da shakku a kan yadda ya ke gudanar da ayyukan sa.

Sanarwar ta kara da cewa, Barista Muhuyi Rimin Gado zai koma bakin aikinsa ne nan take.

Leave a Reply