Home Labaru Abba Kyari Zai Koma Bakin Aiki Bayan Coronavirus

Abba Kyari Zai Koma Bakin Aiki Bayan Coronavirus

880
0

Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Aba Kyari, wanda ya kamu da cutar coronavirus, ya ce nan ba da jimawa ba zai koma bakin aikinsa.

Abba Kyari, ya ce bayan kamuwarsa da coronavirus, ya killace kansa kuma ya ci gaba da yin aiki daga gida tare da kiyaye matakan da gwamnati da hukumomin lafiya suka bayar ga masu cutar.

Ya ce duka da cewa cutar ba ta ci karfinsa ba kuma ba ya nuna alamarta kamar saurana masu catar, amma zai koma Legas domin a ci gaba da duba lafiyarsa daga aljihunsa.

Babban jami’in gwamnatin ya ce ya zabi kula da lafiyarsa daga aljihunsa ne domin saukaka wa cibiyoyin lafiyan gwamanti, da ke aiki ba dare ba rana a yaki da cutar coronavirus da sauran matsalolin rashin lafiya a fadin kasar.

Abba Kyari ya kuma yaba wa ma’aikatan ofishinsa bisa jajircewarsu, tare da jinjina ga ma’aikatan lafiya da ke kan gaba wurin yaki da coronavirus a Najeriya.

Tuni dai Abba Kyari ya isa birnin Legas a cikin wanin jirgin daukar marasa lafiya.