Home Labarai 2027: Ecowas za ta Samar da Kuɗin Bai-Ɗaya

2027: Ecowas za ta Samar da Kuɗin Bai-Ɗaya

112
0
download (6)
download (6)

Ƙungiyar ci gaban tattalin arziƙin yankin Afirka ta Yamma (ECOWAS) ta ƙara zabura domin tabbatar da samar da kuɗi na bai-ɗaya a tsakanin ƙasashenta mai suna ACO.

Ƙasashen ƙungiyar sun cimma wannan yarjejeniyar ce a babban taron da suka yi karo 66 a Abuja.

Asali, ƙasashen ƙungiyar sun ɗauki haramar ƙaddamar da kuɗin ne a shekarar 2020, amma annobar covid-19 ta kawo tsaiko.

Amma yanzu, sun yanke shawarar ƙaddamar da kuɗin a shekarar 2027, kamar yadda Channels ta ruwaito.

Ƙungiyar ta ce kuɗin na bai-ɗaya zai taimaka wajen inganta harkokin kasuwanci, da tattalin arzikin ƙasashen.

Leave a Reply