Home Labaru 2023: Kotu Ta Umarci INEC Ta Ci Gaba Da Rajistar Masu Zabe

2023: Kotu Ta Umarci INEC Ta Ci Gaba Da Rajistar Masu Zabe

34
0

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta ba Hukumar Zabe ta Kasa umarnin ta gaggauta ci-gaba da shirin yi wa masu zabe rajistar zaben shekara ta 2023.

Umarnin kotun dai, ya nuna hukumar zabe za ta koma ta ci-gaba da shirin ne har sai ya rage kwanaki 90 kafin zaben shekara ta 2023.

A cikin hukuncin da ya yanke, Alkalin kotun Mai Shari’a Inyang Ekwo, ya ba hukumar zaben umarnin ta tabbatar ba ta hana duk ‘yan Nijeriyan da shekarun su ya kai 18 damar yin rajistar ba.

Ya ce hakki ne a kan hukumar ta tabbatar ta yi shirye-shiryen da su ka kamata daidai da doka wajen gudanar da shirin.