Home Labaru Ɗaukar Nauyin Ta’addanci: Kotu Ta Tsayar Da Ranar Gurfanar Da Mutane 400...

Ɗaukar Nauyin Ta’addanci: Kotu Ta Tsayar Da Ranar Gurfanar Da Mutane 400 Da Ake Zargi

34
0

Wata babban kotun tarayya da ke Abuja ta tsayar da ranar 17 ga watan Satumban 2021 domin gurfanar da mutane 400 da ake zargi da daukan nauyin ta’addanci a Nigeria, inda aka ruwaito cewa Mai shari’a Anwuli Chikere ne zai saurari karar a kotun ta taryya.


Fadar shugaban kasa ta sanar a watan Maris cewa ta kama wadanda ake zargin da hannu wurin daukan nauyin ta’addanci ta hanyar taimakawa ‘yan Boko Haram samun kudade, wanda galibinsu ‘yan canji ne.
Wasu ‘yan Nigeria daga Hadadiyar Daular Larabawa ta UAE tare da taimakon ‘yan canjin suna tura wa ‘yan ta’addan na Boko Haram kudade a cewar wani rahoto na Daily Trust.


Attoni Janar kuma Ministan Shari’a na kasa, Abubakar Malami (SAN) ya sanar da cewa an kammala shiri don gurfanar da wadanda ake zargin wadanda jami’an yan sandan farar hula SSS suka kama su tare da musu tambayoyi.
Mutanen kasa sun bayyana damuwarsu kan jinkirin da ake yi kafin fara shari’ar inda lauya mai kare hakkin bil adama, Femi Falana (SAN) ya rubuta wasika ga Malami yana neman a bawa Attoni Janar na jihohi ikon yin shari’a tare da hukunta wadanda aka samu da laifin.