Home Labarai Ɗanyen Man Nijar: An Fara Aiki Daga Gaɓar Ruwan Benin

Ɗanyen Man Nijar: An Fara Aiki Daga Gaɓar Ruwan Benin

343
0
niger benin pipeline oil
niger benin pipeline oil

Rahotanni na nuni da cewa an dawo da aikin ɗaukar ɗanyen man Jamhuriyar Nijar ta bututun da aka shimfiɗa zuwa Jamhuriyar Benin,

lamarin da ke alamta kawo ƙarshen tankiya tsakanin ƙasashen biyu.

Radio France Internationale ta ruwaito cewa tun a ranar Juma’a da ta gabata wani jirgin ruwan dakon mai ya isa a gabar tekun Kwatano saboda wannan dallili.

Isowar wannan jirgin ruwa mai suna Aura M, wadda ke sagale da tutar kasar Liberia na nuni da sake ƙaddamar da aikin tura ɗanyen man Nijar daga Benin.

Yawan man da za a ɗiba dai ya kai ganguna miliyan ɗaya, wato kusan daidai da yadda lodin farko da da Benin ta bada damar yi a ranar 19 ga watan Mayu.

A wannan Asabar, rahotanni sun ce an riga an gama loda wannan jirgin ruwa da ɗanyen mai, wanda kuma ana sa ran zai bar gabar ruwa a wannan Litinin.

A farkon watan Yunin wannan shekarar ce aka shiga tankiya  tsakanin Jamhuriyar Nijar da Benin,

biyo bayan kama wasu yan Nijar 5 da ke aiki kan wannan bututu a yankin Sèmè-Podji,

waɗanda mahukuntan Benin suka ce sun shigo ƙasar ba bisa ka’ida ba, lamarin da ya kai ga dakatar da aikin tura ɗanyen man.

Leave a Reply