Dan takarar gamnan jihar Ogun na Jam’iyyar PDP a zaɓen shekara ta 2023 Ladi Adebutu, ya isa kotun sauraren kararrakin zaɓen jihar da shaidu har guda dubu 8.
Ladi Adebutu dai ya na ƙalubalantar nasarar da Dapo Abiodun ya samu a zaɓen Gwamnan Jihar da aka gudanar ranar 18 ga watan Maris da ya gabata.
A kwafin ƙarar da ya shigar, ɗan takarar ya ce ya shigar da ƙarar ne saboda ya na zargin ba a bi Dokar Zaɓe ta Nijeriya ba yayin zaɓen.
Lauyan Ladi Adebutu, Goddy Uche ne ya gabatar da shaidun a gaban kotun da ke zama a Kotun Majistare da ke Isabo a birnin Abeokuta, inda ya roƙi kotun ta karɓi hujjojin sannan ta yi amfani da su.
Sai dai lauyan Gwamna Abiodun, Kehinde Ogunwunmiju, ya yi kira ga kotun ta yi fatali da shaidun saboda ba su bi ƙa’idojin da ya kamata ba, inda daga nan Mai Shari’a Hamidu Kunaza ya ɗage ci-gaba da sauraren ƙarar zuwa ranar Alhamis, 6 ga watan Yuli.