Ƙungiyar ma’aikatan kotuna ta Nijeriya JUSUN, ta ce ta
yanke shawarar shiga yajin aikin da ƙungiyar ƙwadago ta
Nijeriya NLC ta kira daga ranar Laraba mai zuwa.
Matakin dai ya na zuwa ne, domin nuna rashin amincewa da cire tallafin man fetur da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta yi.
Mataimakin sakataren kungiyar na ƙasa Barista Saidu Magaji Ƙarƙaku, ya ce sun karɓi wasikar kungiyar NLC kuma su ma za su rufe kotuna.
Shawarar ƙungiyar dai ya na zuwa ne, bayan rahotanni sun ambato NLC na cewa ta rubuta wasiƙa domin sanar da sauran rassan ta musamman ƙungiyar kungiyoyin ASUU da JUSUN game da buƙatar su shiga yajin aikin.
Mataimakin Sakataren kungiyar JUSUN, ya ce sun dauki matakin ne duba da ganin yadda cire tallafin man fetur zai shafi kusan kowanne ɓangare na rayuwar al’umma a Nijeriya.














































