Tsohon babban hafsan tsaron Nijeriya Janar Lucky Irabor mai
ritaya, ya ce samar da tsaro ga babbar ƙasa kamar Nijeriya ba
abu ne mai sauki ba, amma abu ne da za a iya cimmawa.
Janar Irabor ya bayyana haka ne, a wajen taron karramawar barin aiki da aka shirya masa a barikin sojoji na Mogadishu da ke Abuja, inda ya ce akwai jan-aiki a gaban sojojin Nijeriya na ba ƙasar nan tsaron da take buƙata.
Ya kuma bayyana gamsuwa da gudunmuwar da ya bada a aikin soji, ya na mai cewa zai bar rundunar sojin Nijeriya fiye da yadda ya same ta.
Janar Irabor, ya kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya su guji aikata abubuwan da ka iya zubar wa rundunar soji kima, ya na mai cewa rundunar a shirye ta ke domin kawo haɗin kai da zaman lafiya da kuma kare rayukan ‘yan ƙasa.














































