Home Labarai Raddi: Ba a Taɓa Gwamnatin Da Ta Kai Ta Buhari Rashawa Ba...

Raddi: Ba a Taɓa Gwamnatin Da Ta Kai Ta Buhari Rashawa Ba – Naja’atu

534
0

Daya daga cikin jami’an Hukumar Dauka da Ladabtar ‘Yan sanda Naja’atu Mohammed, ta soki lamirin Shugaba Muhammadu Buhari a kan yafe wa Joshua da Jolly Nyame da ya yi.

A wata tattaunawa da manema labarai, Naja’atu Mohammed ta
ce ya dace shugaba Buhari ya gane cewa dukiyar Nijeriya ba ta
shi ba ce.

Ta ce gwamnoni ya kamata a ce sun yafiyar, domin a jihohin su
aka aikta rashawar ba matakin tarayya ba, saboda kundin tsarin
mulki ya bada hurumin yafiya ne ga jihohin da aka aikata
laifuffukan.

Naja’atu Mohammed, yafe wa tsofaffin gwamnonin ya nuna
cewa ba a shirya kawo karshen cin hanci da rashawa a Nijeriya
ba.

Ta ce an zabi shugaba Buhari ne don ya yi yaki da cin hanci da
rashawa, amma yanzu shi ya ke yafe wa masu aikata laifin, ta na
mai cewa hakan ya nuna cewa shugaba Buhari ba abin
amincewa ba ne, domin Satar da ake tafkawa a gwamnatin sa ta
zarce tunani.

Leave a Reply