Gwamnatin Najeriya za ta rabawa manoma Irin alkama mai jure zafin rana da yawan sa ya kai tan dubu 1 da 500 a bana, ƙarƙashin shirin tallafawa aikin noma kashi na 1.
Shugaban shirin a matakin ƙasa, Ibrahim Mohamed Arabi ne ya bayyana haka, a ziyarar da ya kai wani kamfanin takin zamani a ƙaramar hukumar Madobin jihar Kano.
Ibrahim Arabi, ya ce sabon Irin zai taimaka wajen magance ƙarancin alkama da tsadar ta, yayin da a gefe guda zai tallafawa ƙananan manoma,
ya ƙara da cewa kamfanin Al-Yuma da ke samar da Iri, da taki, da sauran kayayyakin noma na Jihar Kanon ne zai samar da Irin alkamar.
A zantawar sa da manema labarai, shugaban ƙungiyar manoman Najeriya AFAN, Dr Farouk Rabi’u Mudi, ya ce matakin zai yi tasiri matuƙa wajen kawo cigaban fannin noma musamman na alkama.
Dr Farouk ya kuma ce cigaban zai inganta yanayin yadda ake samar da alkama, kasancewar ita bata fitowa a lokacin zafi, sai dai samar da wannan Iri mai jure zafi zai sanya a samu wadatar ta.