Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya wato INEC ta musanta rahotannin da ake yaɗa cewa tana bincike kan ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu.
A ranar Juma’a ne wata sanarwa da aka alaƙanta da hukumar ta INEC ke cewa hukumar na gudanar da bincike kan wani lamarin kotu na 1993 inda gwamnatin Amurka ta ƙwace wasu kuɗaɗe daga hannun Tinubu.
Sai dai cikin wata sanarwa a ranar Asabar, INEC ta ce labarin ba gaskiya bace na ƙanzon-kurege ne.
INEC ta ce wata sanarwa da ta dinga waɗari a shafukan sada zumunta cewa INEC ta ƙaddamar da bincike kan wani laifi a Amurka da ya ƙunshi wani ɗan takarar shugaban ƙasa a babban zaɓe mai zuwa domin tantance ko ya karya dokokin dokar zaɓe ta 2022 kanzon Kurege ne.
INEC ta ce ko shakka babu sanarwar ba daga gareta take ba domin ita ba ta gudanar da wani bincike a kan wani dan takara, surutu ne kawai irin na masu neman tayar da zaune tsaye.














































