Majalisar wakilai ta amince da garambawul a kundin zaɓe na shekara 2022, domin a ba masu rike da madafun iko damar shiga tarurrukan jam’iyyu da zaɓen fidda gwani.
Wata ta ce, Majalisar ta amince da gyaran ne a sashe na 84, bayan yin nazari a kan kudiri dokar.
Dan majalisa Abubakar Hassan Fulata ne ya ɗauki nauyin gabatar da kudirin a zauren majalisar aka kuma amince da shi.
Matakin dai ya na zuwa ne, sa’o’i 24 bayan majalisar Dattawa ta amince da yi wa kundin dokar garambawul.














































