Home Labarai Magance Fasa-Ƙwauri: NSA Ya Ce Cire Tallafin Man Fetur Ya Taimaka

Magance Fasa-Ƙwauri: NSA Ya Ce Cire Tallafin Man Fetur Ya Taimaka

349
0
National Securuty Adviser Nuhu Ribadu e1716792973301
National Securuty Adviser Nuhu Ribadu e1716792973301

Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu ya ce cire tallafin man fetur da shugaban kasa Bola Tinubu ya yi ya kawo karshen fasa-kwaurin man fetur da ake yi a fadin kasa.

Nuhu Ribadu ya bayyana haka ne a nan Abuja a taron da ake yi na Kwanturola Janar na Hukumar Kwastam, inda ya kara da cewa Najeriya na tallafawa kasashe makwabta ne kadai saboda fasakwaurin da ake yi a kan iyakokin kasa.

 NSA ya alakanta dimbin yawan man fetur a kasar nan da tsarin tallafin da suke amfana da shi.

Ya ce Najeriya ce kasa daya tilo a duniya da kowa ya zama dan kasuwan mai saboda tallafin man dana ana iya kirga kusan gidajen mai guda 100 daga Abuja zuwa Kaduna kadai, Saboda biyan tallafin amma yanzu ya kare.

Leave a Reply