Home Labarai Kakar Bana: An Ci Chelsea Duk Da Ƴan Wasa 11 Da Ta...

Kakar Bana: An Ci Chelsea Duk Da Ƴan Wasa 11 Da Ta Ɗauka

355
0
2024 08 18T173341Z 1533800928 UP1EK8I1CS390 RTRMADP 3 SOCCER ENGLAND CHE MCI REPORT
2024 08 18T173341Z 1533800928 UP1EK8I1CS390 RTRMADP 3 SOCCER ENGLAND CHE MCI REPORT

Manchester City ta je ta doke Chelsea 2-0 a wasan makon farko a Premier League da suka kara ranar Lahadi a Stamford Bridge.

Shi ne karon farko da sabon koci, Enzo Maresca ya ja ragamar Chelsea, wadda ta ɗauko daga Leicester City a kakar da ta wuce.

Chelsea, wadda ta yi ta shida a bara ta raba gari da koci, Mauricio Pochettino, sannan ta maye gurbinsa da Marresca.

Minti na 18 da take leda ne City ta fara cin kwallo ta hannun Erling Halland – na 106 kenan da yake da hannu a wasa na 100 a kungiyar Etihad,

wanda ya ci 91, sannan ya bayar da 15 aka zura a raga.

Tun daga kakar 2022-23, Erling Haaland ya ci ƙwallaye da yawa a Premier League cikin watan Agusta sau 13 fiye da yawan na Chelsea 11 da Manchester United guda tara.

Daga baya ne City ta kara na biyu ta hannun Mateo Kovacic, saura minti shida a tashi daga fafatawar ta hamayya.

Leave a Reply